Dakarun Yaman sun kai Hare-haren kan wani Jiragin ruwan daya kutsa cikin tekun Bahar Maliya

 


Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Janar Yahya Saree ya sanar a ranar Juma'a da Dare cewa an kaddamar da hare-hare da Jirage marasa matuka da makamai masu linzami kan wani jirgin ruwa a tekun Bahar Maliya da mashigin Bab al-Mandeb.


A cewar Al-Masirah, Janar Saree ya ce sojojin ruwa, da kuma Sojojin Jirage marasa matuka da na makami mai linzami sun gudanar samame na hadin gwiwa kan jirgin (Charysalis) a tekun Bahar Maliya da mashigin Bab al-Mandab.


Kakakin rundunar sojin Yaman ya kara da cewa, wannan harin ya faru ne bayan da jirgin ruwan ya yi biris da dokar hana shiga tashar jiragen ruwa na Falasdinu da aka mamaye.


Ya kara da cewa "Ayyukan na Dakarun Yaman za su ci gaba da gudana har sai gwamnatin sahyoniyawa ta daina kai hare-haren wuce gona da iri a kan Gaza, sannan kuma ta ɗage duk wani shingen da aka yi wa al'ummar Palastinu a wannan yanki."


A karshe General Saree ya jaddada cewa a shirye dakarun kasar Yemen suke wajen aiwatar da bukatun al'ummar kasar domin dakile ayyukan makiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post