Hezbollah ta Ƙera Jirage Marasa Matuƙa Da ba Za'a Iya Gano su ba Cewar Wani Jami'i

 


Nawaf Al-Mousavi, wanda shi ne mai kula da albarkatu da kuma kan iyakoki a kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a da Dare inda yake cewa, kungiyar ta kera jirage marasa matuka wadanda ba za a iya gano su ba sannan kuma ba Za'a iya harbo su ba.


A cewar Al-Mayadeen, Al-Mousavi a wata hira da wannan tashar ta Lebanon ya ce, "Abin da muka yi amfani da shi a wannan yakin a cikin watanni 10 da suka gabata ba shi ne kawai abin da muke da shi ba."


Mai kula da albarkatu da iyakoki a kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, a yau gwamnatin Sahayoniya tana maimaita irin kura-kuran da ta yi na yakin kwanaki 33 (a shekara ta 2006).


Ya bayyana cewa shirun da kasashen Larabawa suka yi a kan abubuwan da suke faruwa a Gaza ba abin da za a yi musu uzuri ba ne.


Jami'in na Hizbullah ya kara da cewa, "Yin Nasara akan Hamas fa baza ya amfanar da gwamnatocin kasashen larabawa ba."

Post a Comment

Previous Post Next Post