Jiragen Yaƙin Isra'ila Sun Sake Kai Hari a Babban Birnin Syria

 


Sojojin yahudawan sahyoniya sun sake kai hari kan birnin Damascus da makamai masu linzami, kamar yadda majiyoyin yada labarai na Syria suka rawaito a safiyar Lahadi.


A cewar IRNA, inda ta nakalto daga SANA, Dakarun tsaron sararin samaniyar Siriya sun kakkabo makaman roka da jiragen yakin gwamnatin sahyoniyawan suka harba tare da harbo mafi yawa daga cikinsu.


Kawo yanzu dai babu wani rahoto da ke nuna cewa akwai yiyuwar barna ko asarar rayuka daga wadannan hare-haren.


 Isra'ila ta kai irin wadannan hare-hare da dama a kan Syria da suka hada da Damascus babban birnin kasar da sauran wurare cikin shekaru ashirin da suka gabata.


 Gwamnatin Syria ta gabatar da korafe-korafe da dama ga Majalisar Dinkin Duniya da komitin sulhu, tana mai zargin gwamnatin Isra'ila da keta hurumin kasarta, da kuma samar da kungiyoyin 'yan ta'adda da irin wadannan hare-hare don kawo cikas ga zaman lafiyar kasar ta Larabawa."

Post a Comment

Previous Post Next Post