Kamfanin yada labarai na kasar Australia ya sanar da cewa, ma'aikatar aikin gona ta kasar Australia ta kauracewa ba da izinin jigilar naman dabbobi daga Australia zuwa "Isra'ila" saboda fargabar hare-hare daga Yemen.
Jigilar shanu 4,000 zuwa Isra'ila ya samu jinkiri na tsawon wata guda, inda ake jiran amincewar hukumomin Australia na barin tashar jiragen ruwa na Fremantle.
Kamfanin ya bayyana cewa, sakamakon barazanar da kasar Yaman ta yi, shanu 2,728 ne akayi jigilar su zuwa Isra'ila a bana, idan aka kwatanta da fiye da 70,000 a bara.
Shugaban sashen kiwon dabbobi na WAFarmers Geoff Pearson ya bayyana cewa akwai tsananin bukatar tumaki da shanu a kasar Isra’ila a halin yanzu, inda ya tabbatar da cewa farashin Jan nama ya yi tashin gwauron zabi kuma ana fama da karancin Jigilar su.
Kamfanin yada labaran kasar Australia ya yi nuni da abinda ya kira matsalolin tsaro daga Yemen da kuma tekun Red Sea na hana jigilar dabbobi daga Fremantle na kasar Austireliya zuwa Isra'ila, inda ya yi nuni da cewa, jirgin ruwan da ake fitarwa zuwa kasashen waje ya shafe makwanni hudu yana jiran ya samu izinin shiga tekun.
Kasar Yemen ta sanya dokar hana jiragen ruwa da ke da alaka da Isra'ila, tare da hana su shiga tashoshin jiragen ruwa na Isra'ila, domin nuna goyon baya ga Falasdinawa dake fuskantar kisan kare dangi na tsawon watanni 10. Wannan haramcin ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki, ƙarancin kayayyaki, da kuma rufe tashar jiragen ruwa a Isra'ila.
Yakin da Isra'ila ke kaiwa Gaza wanda ya fara a ranar 7 ga watan Oktoba, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 39,000 galibi mata da kananan yara, tare da jikkata sama da 90,000, tare da raba da dama daga gidajensu.
