Isra'ila ta Kai Hare-hare a Wasu Garuruwa a Kudancin Lebanon

 


Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta sake kaddamar da wasu sabbin hare hare kan kasar Labanon bisa da'awar mayar da martani kan 'yan gwagwarmayar Hizbullah, inda saboda da taurin kai ta ɗaurawa ƙungiyar gwagwarmayar alhakin wani hari na baya-bayan nan kan yankin Golan na kasar Siriya da Isra'ila ta mamaye.


Takai hare-haren ne kan garuruwan dake kudancin Lebanon da suka haɗa da Houla, Markaba, Aita al-Shaab, Khiam, Shaheen, Yaroun, Mays al-Jabal, Kfarkela, da Bourj al-Shamali a ranar Litinin, kamar yadda kafafen watsa labaran Lebanon suka ruwaito.


Wannan dai shi ne karo na biyu da haramtacciyar gwamnatin ke kai hare-hare kan Lebanon tun ranar Asabar, lokacin da wani harin roka ya kashe akalla mutane 12 a tuddan Golan na kasar Syria da suka mamaye.


Jami’an Isra’ila da suka hada da firaministan kasar Benjamin Netanyahu, da ministan harkokin wajen Isra’ila Katz, da ministan kudi Bezalel Smotrich, da mai magana da yawun sojin kasar Daniel Hagari, sun dage cewa kungiyar Hizbullah ce ke da alhakin kai harin, kuma sun yi alkawalin daukar alhakin kai harin.


Sai dai kuma Dakarun na Musulunci sun musanta sa hannun su a lamarin.


 A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan harin, kungiyar Hizbullah ta jaddada cewa, "Kungiyar Gwagwarmayar ba ta da alaka da lamarin, kuma ta musanta dukkan zarge-zargen karya game da hakan."


Wasu rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiwuwar fashewar da ta afku a kauyen na Syria ya faru ne sakamakon wani makami mai linzami da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta harba da ake kira da makami mai linzami na Iron Dome.


 Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila wadda ta yi yaki sau biyu a kan kasar Labanon a shekarun 2000 da 2006, ta yi ta yin barazana a cikin watanni 10 da suka wuce, na sake kai wa kasar Labanon hari a cikin wani farmakin soja na bai daya.


Jami'an Isra'ila kuma sun sha yin barazanar cewa za su "kona Lebanon, su lalata ta, da mayar da ita zuwa zamanin dutse."


Kungiyar Hizbullah dai na daukar matakin ramuwar gayya ta hanyar kai hare-hare da makami mai linzami kan sansanonin soji da ke kwance a sassan arewacin yankunan Falasdinawa da ta mamaye.


Har ila yau kungiyar ta yi alkawarin kare kasar da dukkan abinda ta mallaka yayin wani yaki da Isra'ila.

Post a Comment

Previous Post Next Post