Dakarun Iraqi sun Kai Harin Jirgi Mara Matuƙi a Eilat

 


Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a Iraki ta ce ta kai hari tashar jiragen ruwa ta Eilat (Umm al-Rashrash) da ke yankunan da aka mamaye da jirage marasa matuka.


A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, kungiyar gwagwarmayar ta ce mayakanta sun kaddamar da harin ne domin yaƙar mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma mayar da martani ga kisan gillar da Isra'ila ke yi wa fararen hulan Falasdinawa.


Ba'a daɗe ba, kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan suka ba da rahoton kunna sanarwar gargadi ta sararin samaniyar tashar jiragen ruwa ta Eilat a kudancin Falasdinu da ta mamaye.


A 'yan watannin baya-bayan nan kungiyar gwagwarmayar Musulunci a Iraki ta kai hari kan wasu muhimman sansanonin Isra'ila a Eilat.


Kungiyar ta Islama ta gargadi gwamnatin 'yan mamayan kan ƙarin wasu munanan hare-hare idan ta ci gaba da yaƙin da take yi na kisan kare dangi a kan al'ummar Falasɗinu a zirin Gaza.

Post a Comment

Previous Post Next Post