Sojojin Isra'ila 14 ne Suka Jikkata a Cikin Sa'o'i 24 da Suka Gabata


Sojojin Isra'ila 14 ne suka samu raunuka a cikin sa'o'i 24 da suka gabata a yayin yakin da ake ci gaba da gwabzawa a zirin Gaza, kamar yadda kafafen yada labarai suka Ruwaito.


Sanarwar da Rundunar Sojin Isra'ila ta fitar ta ce sojojin Isra'ila 3,703 ne suka jikkata tun bayan barkewar yakin Gaza, yayin da 1,878 daga cikin su sun samu raunuka ne ta hare haren da ake kaiwa ta kasa a yankin, kamar yadda kafafen yada labaran Larabawa suka rawaito.


Rundunar sojin Isra'ila ta kara da cewa jami'ai da sojoji 254 na ci gaba da jinya bayan da suka samu raunuka a fada da kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu, yayin da 32 daga cikinsu sun samu munanan raunuka.


Kungiyar yahudawan sahyoniya dai na boye irin hasarar da akeyi masu na masu raunuka, wadanda aka kashe da sauransu a yaƙin, amma duk da haka abin yaƙi ɓoyuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post