Dakarun Muslunci na kasar Labanon sun sake kai hari kan cibiyoyin Tattaruwar Sojoji guda 2 na Gwamnatin Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila da ke yankin Arewacin Falastinu da ta mamaye.
Kafafen yada labaran Hezbollah sun sanar a cikin wata sanarwa cewa, mun kai hari kan tarurrukan sojojin mamaya a yankin Shlomi da makami mai linzami da ya dace.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Labanon ta kara da cewa: An kai wannan harin ne domin tallafa wa al'ummar Palastinu masu tsayin daka a yankin Zirin Gaza da kuma goyon bayan gwagwarmayar Falasdinawa masu jaruntaka da mutunci..
A cewar rahoton, an kuma kai wannan harin ne a matsayin martani ga hare-haren da Isra'ila ta kai kan kauyuka da gidajen zama a kudancin kasar Lebanon, ciki har da garin "Al Naqourah", wanda yahudawan sahyuniya suka kai wa hari a baya-bayan nan.
