An yi Bukin Tunawa da Marigayi Imam Khomeini a Kasar Birtaniya


An gudanar da bikin cika shekaru 35 da wafatin marigayi Imam Khumaini a babban birnin kasar Birtaniya.


Shuwagabannin cibiyoyin addinin musulunci, ma'aikatan hukumomin Iran a Birtaniya, da ma'aikatan ofishin jakadancin Iran dake birnin London da kuma wasu Iraniyawa mazauna birnin Landan ne suka halarci bikin da aka gudanar a ranar Litinin da yamma agogon kasar.

 Jami'in hulda da jama'a na Iran a London Ali Matinfar ne ya dauki nauyin bikin.


 Da yake jawabi a wajen bikin zagayowar ranar wafatin, Matinfar ya ce marigayi Imam tun farkon shekarun juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979 ya jaddada muhimmancin mai da hankali kan batun Falasdinu, da amincewa da Isra'ila a matsayin gwamnatin mamaya da kuma goyon bayan Falasdinawa da ake zalunta.

Jami'in diflomasiyyar ya kara da cewa a lokacin rayuwarsa, Imam ya tunatar da al'ummar musulmi kan lamarin.


 Shekara guda bayan juyin juya halin Musulunci a Iran Imam ya bayyana ranar Juma'ar karshe ta azumin watan Ramadan a matsayin ranar Qudus;  kuma ana gudanar da ranar a dukkan kasashe a kowace shekara tare da halartar jama'a a fadin duniya, in ji Matinfar.


Ya ci gaba da cewa Imam Khumaini ya nanata cewa wajibi ne al'ummomi su bayyana irin zaluncin da ake yi wa Falastinawa da laifukan 'yan mamaya domin nuna al'amarin Falasdinu  raye har abada.


Daga karshe Matinfar ya tuna da shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi da tawagarsa da suka hada da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian da suka yi shahada a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin kasar Iran a ranar 19 ga watan Mayu.

Post a Comment

Previous Post Next Post