Babban kwamandan dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Hossein Salami, ya ce za a hukunta Gwamnatin Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila saboda "Jini Mai Tsarki da Suka Zubar."
Manjo Janar Salami ya mika ta'aziyyarsa na shahadar wani mai ba da shawara kan harkokin soji na IRGC Saeed Abiar wanda ya yi shahada a harin da yahudawan sahyuniya suka kaddamar kan birnin Aleppo na kasar Siriya da yammacin jiya Lahadi.
Hakika za a tuna da irin ƙoƙari na wannan jarumin da ya sadaukar da rayuwarsa don kare tsarin Musulunci da kuma tsayin dakan sa da kuma kyakkyawan aikin sa, inji Babban kwamanda.
Haƙiƙa Ayyukan shahidai za su zaburar da mayaƙan al'ummomi masu zuwa, in ji shi.
A ranar Talata ne aka gudanar da jana’izar Abiar a hubbaren Sayyida Ruqayya (AS), ‘yar Imam Husaini – limamin Shi’a na uku.
Har ila yau, a jiya a birnin Tehran, al'ummar Iran sun yi bankwana da Marigayin Mayaƙin a bikin da aka gudanar wanda dimbin Jama'a suka halarta.
Muna rokon Allah daya Karɓi Shahadarsa.
