An kama Jami'in Mossad a Arewa Maso Yammacin Iran


 Iran ta kama wani dan leken Asiri da ke Aiki da hukumar Mossad ta Isra'ila a lardin Ardabil da ke arewa maso yammacin kasar.


Ma’aikatar leken asiri ta dade tana neman dan leken asirin, kuma daga karshe ofishin mai gabatar da kara a lardin Ardabil ne ya kamashi a yau Laraba.


Wakilin na Mossad ya yi tattaki zuwa wasu larduna da dama da nufin boyewa da kuma manufarsa ta karshe ta barin kasar, saidai kuma daga zuwan sa lardin Ardabil aka kama shi a wani samame na ba-zata.


 A cewar ofishin mai shigar da kara na lardin, wakilin ya yi mu'amala da manyan jami'an Mossad ta hanyar ɗaya daga cikin shafukan sada zumunta na yanar gizo, inda yake tattara musu bayanai daga cikin kasar da sunan yin aikin edita.


Dan leken asirin da aka kama ya fito ne daga kudancin Iran, wanda Mossad ta cire asusun shi da kuma bayanan da ke da alaka da shi nan da nan bayan kama shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post