Mayakan Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Shiga Cikin Yankunan da Aka Mamaye


Rahotanni sun ce mayakan gwagwarmayar Falasdinawa sun kutsa cikin yankunan da Isra'ila ta mamaye a yau Alhamis.


Kamfanin dillancin labaran IRNA ya ruwaito cewa, ya nakalto daga tashar talabijin ta Al Mayadeen cewa, a yau Alhamis sojojin kasar Isra'ila sun sanar da cewa, an samu wani lamari na tsaro a kan iyakar Gaza da kuma yankunan da aka Mamaye.


Gidan rediyon sojojin yahudawan sahyoniya ya bayar da rahoton cewa, tawagar mayakan gwagwarmayar Palastinawa sun kutsa cikin yankunan da aka mamaye daura da mashigar Karam Abu Salem a Rafah kimanin sa'o'i biyu da suka gabata.


Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da barkewar rikici tsakanin sojojinta da mayakan Falasdinawa a wannan yankin, sannan ta kuma amince cewa sojojinta biyu sun jikkata a wannan rikici.


Kungiyar sa ido ta Isra'ila ta hana buga cikakken bayanan wannan gazawar leken asiri.

Post a Comment

Previous Post Next Post