Kafofin yada labaran Yemen sun ruwaito a ranar 6 ga Yuni, 2024, cewa kawancen Amurka da Birtaniya sun kai hare-hare ta sama a yammacin Yaman, inda suka hari yankunan bakin teku.
Cewar Al-Masirah TV, Jiragen yakin Amurka da na Birtaniyya sun yi ruwan bama-bamai a gundumar Al-Lahiya da ke lardin Hudaydah, yayin da tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, rundunar kawancen ta kai hari kan wasu jiragen ruwan kamun kifi guda biyu a yankunan Al-Khawba da Al-Lahiya da ke gabar teku.
A nasa martanin Sayed Abdulmalik Badruldeen Al-Houthi jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yaman ya sha alwashin ci gaba da tallafawa Gaza tare da gargadi kan hada kai da Amurka. Ya kuma yi alkawarin mayar da martani ga duk wani harin wuce gona da iri kan kasar Yemen, tare da bayyana cewa hare-haren ba za su hana su cimma matsayarsu ba.
A baya dai sojojin kasar Yemen sun kai hari kan jiragen ruwa na Amurka da Birtaniya da kuma Isra'ila a tekun Bahar Maliya da mashigin Bab al-Mandab domin goyon bayan gwagwarmayar Falasdinawa a Gaza. Sun sha alwashin ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke zuwa Isra'ila har sai an daina kai hare-hare a Gaza.
