Imam Khamenei: Guguwar Al-Aqsa Za ta kai ga Kawar da Isra'ila, Hamas da Hizbullah ne za suyi Nasara


Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Imam Sayyed Ali Khamenei ya tabbatar a yau Litinin cewa Guguwar Al-aqsa ta Falasdinawa ta Saka Isra'ila a cikin Wani Irin Tarkon da Baza su iya Kuɓucewa ba.


A jawabin da Jagoran ya gabatar a wajen zagayowar cika shekaru 35 da wafatin Imam Khumaini, Imam Khamenei ya yi duba da cewa, an gudanar da wannan guguwar ta Al-aqsa a kan "Isra'ila" a daidai, wanda aka sanya Haramtacciyar Ƙasar a kan hanyar da ba za ta kai ko ina ba sai Rugujewa da Ƙarewa.


Ya jaddada cewa "kasashen yammacin duniya duk sun furta cewa babu wata mafita ga 'Isra'ila' bayan harin Guguwar Al-aqsa."


"Imam Khamenei ya bayyana cewa harin Guguwar Al-Aqsa ya yi mummunar illa ga yahudawan sahyoniyan, wanda ba za su farfado daga gare shi ba, ya kuma yi nuni da cewa, wannan farmakin ya dakile duk wani makircin Isra'ila a yankin, ya yi gargadin cewa Isra'ila na da cikakken shiri na sauya alkiblar yankin, amma Guguwar Al-Aqsa ta yi mummunar naushi gare su, wanda ya tura su zuwa Durkushewa."


"Amurka da kasashen Yamma suna goyon bayan sahyoniyawan, amma kowa yasan cewa babu wata hanyar kubuta daga wannan tarkon data fada a Gaza," in ji shi.


 Yayin da yake kira ga al'ummar yankin da kada su sanya fatansu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, Imam Khamenei ya nakalto wani masanin tarihi na "Isra'ila" yana cewa yahudawan sahyoniya na rugujewa kuma "Isra'ila" ta fara shan wahala a farkon karshenta.


Jagoran ya kara da cewa: "Wata takwas bayan guguwar ta Al-Aqsa, kungiyar sahyoniyawan ba ta cimma wani burinta ba," in ji Jagoran yana mai cewa "Hare-haren wuce gona da iri da Yahudawan Sahayoniya suka kai a Gaza wani martani ne mai matukar tayar da hankali kan gazawar shirinta na yankin."


 Jagoran ya ci gaba da cewa: Daya daga cikin Nasarorin Guguwar ta Al-Aqsa ita ce, lamarin Palastinu ya koma batu na daya na duniya baki daya.


Ya kara da cewa, "Duk da yawan shahidai, wadanda abin ya shafa da kuma barna, al'ummar Palastinu na ci gaba da turjiya a gaban 'Isra'ila'. Falasdinawa dubu 40 ne suka yi shahada a Gaza, kuma wannan shi ne kudin da al'ummar Palasdinawa suke biya a hanyar tsira da 'yantar da kasarsu."


Imam Khamenei ya yi Allah wadai da goyon bayan da kasashen yammacin duniya ke yi na kisan kiyashi da Isra'ila ke yi a Gaza, Imam Khamenei ya jaddada cewa, "Amurka tana tsaye a gaban yarjejeniya ta duniya kuma an tilasta ta yin aiki mai tsanani."


Ya kara da cewa "Hukumar yahudawan sahyoniya ta shiga wani rufaffen rami kuma ba za ta iya tserewa daga gare shi ba."


A daya bangaren kuma, Jagoran ya tabbatar da cewa "Ƙungiyoyin gwagwarmaya irinsu Hamas da Hizbullah sun fatattaki sojojin 'Isra'ila'.

Post a Comment

Previous Post Next Post