Wani magajin garin Isra'ila ya sallama akan ƙarfin Jirage Marasa Matuka da kuma Makamai Masu Linzami na Kungiyar Gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon, wadanda suka yi mummunar barna a Yankunan Arewacin Isra'ila da ta mamaye.
A cewar wani rahoton gidan talabijin na Al-Mayadeen a ranar Lahadi, shugaban Garin Margaliot, Eitan Davidi, ya amince cewa kungiyar Hizbullah ce take Juya yankunan arewacin Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila.
Jami'in na Haramtacciyar Ƙasar ya kuma bayyana cewa, babu wani wuri da makamai masu linzami na Hizbullah basa zuwa.
Majalisar ministocin Isra'ila ta kasance mai rauni kuma an doke ta, ya kara da cewa majalisar ministocin ta fi ba da muhimmanci ga wanzar da hadin gwiwa fiye da tsaron wadanda ke zaune a arewa.
Jaridar Ynetnews ta ruwaito a yau Lahadi cewa hare-haren da kungiyar Hizbullah ke kaiwa a yankunan arewacin kasar na karuwa sosai, kuma suna amfani da makamai masu linzami masu nauyi.
Kafofin yada labaran Isra'ila a baya sun bayar da rahoton cewa, ko da yake kungiyar Hizbullah na amfani da takaitaccen adadin makamanta wajen yakar Haramtacciyar Gwamnatin, duk da haka hare haren ta na samun nasara sosai.
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kuma sanar da cewa kungiyar Hizbullah ta yi amfani da kashi biyar cikin Dari ne kawai na makamanta a watannin da suka gabata.
Kungiyar Hizbullah ta sanar a jiya Asabar cewa mayakanta sun yi nasarar harbo jirgi maras matuki na hudu na Isra'ila mai suna Elbit Systems Hermes 900 Kochav.
Mayakan kungiyar Hizbullah sun yi artabu da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila a gumurzun da aka gwabza a yankunan arewacin kasar a cikin watannin da suka gabata domin rage matsin lamba kan mayakan Falasdinawa.
