Ƙasar Faransa ta haramtawa kamfanonin Isra'ila halartar bikin baje kolin makamai da masana'antun tsaro "Eurosatory" na bana, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.
A cewar Al Jazeera, sanarwar ta Faransa ta zo ne kwanaki kadan bayan da Isra'ila ta kai hari kan sansanin 'yan gudun hijira a Rafah da ke kudancin Gaza.
Faransa ta haramtawa kamfanonin Isra'ila shiga baje kolin makamai da masana'antun tsaro "Eurosatory" na bana a Villepinte kusa da Paris a wannan watan na Yuni, in ji masu shirya taron da hukumomin Faransa.
Ma'aikatar tsaron Faransa ta ba da shawarar cewa matakin na da nasaba da adawar Paris da ci gaban farmakin da Isra'ila ke kaiwa Rafah a kudancin Gaza.
Sharuɗɗan da zasu sa a bada damar karbar bakuncin kamfanonin Isra'ila a wurin baje kolin basu cika ba, a daidai lokacin da shugaban na Faransa ya yi kira ga Isra'ila data daina gudanar da hare hare a Rafah, kamar yadda ma'aikatar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
