Kasar Chile ta bi Sahun Kasashen da ke Goyon Bayan Shari'ar Kisan Kare Dangi a Kan Isra'ila


Kasar Chile itace ta baya bayan nan da ta shiga Jerin kasashen da ke goyon bayan Afirka ta Kudu da suka shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa ICJ kan kisan kare dangi da Isra'ila ke yi.


Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya ruwaito cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Rasha Tass cewa, shugaban kasar Chile, Gabriel Borich ya sanar a jiya Asabar cewa kasarsa za ta shiga cikin shari'ar kisan kiyashi akan Isra'ila.


 Boric ya bayyana a wani jawabi da ya yi wa ‘yan majalisar cewa ya yi matukar kaduwa da irin barnar da ake yi a Gaza musamman mata da kananan yara. Ya zargi sojojin Isra'ila da yin amfani da karfin tuwo a kan Falasdinawa da ba su ji ba ba su gani ba.


"Wadannan ayyukan suna bukatar al'ummar kasa da kasa da su mayar da martani na dindindin a kansu," in ji shugaban.


Afirka ta Kudu ta kai karar Isra'ila a watan Janairu, inda ta zargi gwamnatin kasar da aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a Gaza inda aka kashe sama da mutane 36,000, galibi mata da yara tun bayan kaddamar da yakinta a ranar 7 ga Oktoba, 2023.


Tun daga watan Janairu, aƙalla ƙasashe 9 suka kai ƙarar a kotun ƙasa da ƙasa a hukumance ko kuma suka bayyana aniyarsu ta yin hakan.


 Chile ita ce kasa ta uku a Kudancin Amurka bayan Nicaragua da Colombia da ke fuskantar kotun ICJ a watan Afrilu.


Ita ma Libya ta gabatar da bukatar shiga tsakani a cikin lamarin. Kasashen Mexico da Brazil da Indonesiya ma sun goyi bayan koken na Afirka ta Kudu.

Post a Comment

Previous Post Next Post