Yemen ta Mayar da Martani kan Harin Amurka, Inda ta Kai Hari Kan Jirgin Ruwan Amurka Mai Dakon Jiragen Yaƙi "USS Eisenhower"


Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yehya Saree ya sanar da cewa dakarun kasar sun kai hari kan jirgin ruwan Amurka USS Dwight D. Eisenhower a tekun Bahar Maliya a matsayin martani ga munanan hare-haren da Amurka ta kai cikin dare a kasar.


"Rundunar makami mai linzami (Missile Force) da sojojin ruwa na Dakarun Yaman sun gudanar da wani harin soji na hadin gwiwa a kan Jirgin Ruwan Amurka 'Eisenhower' mai dakon Jiragen Yaƙi a cikin Bahar Maliya," in ji Saree a cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin.


Ya kuma kara da cewa: “An gudanar da harin ne da makamai masu linzami masu fuka-fukai da na ballistic (Ballistic and Winged Missile), harin yaje inda aka aika shi, Alhamdulillahi.


Saree ya ce wannan wani martani ne ga hare-haren jiragen sama da Amurka da Birtaniya suka kai a fadin kasar, wanda harin an kaishi kan fararen hula "kuma hakan cin zarafin dukkan dokokin kasa da kasa ne kuma cikakken laifin yaki."


 Kakakin Yaman ya sha alwashin cewa kasar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da martani kai tsaye ga duk wani sabon harin da aka kai kan yankunan Yaman, da kuma cewa za ta kai hari akan Amurka da Birtaniya  a cikin Tekun Bahar Maliya da Tekun Larabawa


A ranar Alhamis din da ta gabata shugaban kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya lashi takobin ci gaba da kai hare-haren soji tare da kara murkushe su "cikin inganci da adadi" na goyon bayan Falasdinawa.


 Har ila yau, a ranar Juma'ar da ta gabata, titunan birnin Sana'a, babban birnin kasar Yemen, sun cika makil da tekun al'ummar kasar da ke nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu, tare da yin kira da a ci gaba da nuna goyon baya ga zirin Gaza


A ranar Alhamis ne shugaban Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya lashi takobin ci gaba da kai hare-haren soji na goyon bayan Falasdinawa.


 Har ila yau, a ranar Juma'a ne, titunan birnin Sana'a, babban birnin kasar Yemen, ya cika makil da al'ummar kasar da ke nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu, tare da yin kira da a ci gaba da nuna goyon baya ga zirin Gaza.

Post a Comment

Previous Post Next Post