Duniya na Farkawa Saboda Kisan Kiyashin Isra'ila Inji Sayyid Nasrallah


Shugaban kungiyar Hizbullah, Sayyed Hassan Nasrallah, ya yi Allah wadai da Netanyahu da gwamnatinsa kan mummunan yakin da suke yi, wanda shugabannin kasashen duniya suka yi shiru akai. Duk da haka, wannan ta'addancin nasu yana farkar da duniya.


Sayyid Nasrallah ya kara da cewa: Har yanzu ana ci gaba da gwabza fada a Gaza, inda duniya ta tsaya tana kallo ba tare sun taimaka ba saboda kariyar da Amurka keba Isra'ila, a lokacin da wasu kuma suka daura fatan su ga hukumomin Duniya na dakilewa da kuma bayar da kariya.


Wannan yakin na nuni da makomar kasar Labanon, dukiyarta, da kuma ikonta, inji Sayyid Nasrallah, ya kuma kara da cewa: Wannan yakin kaddara ce garemu baki daya, kuma mun jajirce sosai a kansa, musamman a kudancin kasar Lebanon.


Ya ci gaba da cewa, "Da ace muna Amurka, ko Asia mai nisa, ko wasu yankuna, tallafin kudi da kayan Jin kai na iya wadatar wa; duk da haka, a nan lamarin ya sha bamban, kuma hadin kai da tallafin jin kai kadai ba zai wadatar ba," in ji shi.


Ya ci gaba da cewa, "Mun yi imanin cewa mu ne mafi girman tushe da jam'iyyar siyasa a Lebanon.


Allah ka taimaki 'yan gwagwarmayar Musulunci a duk inda suke.

Post a Comment

Previous Post Next Post