Wakilin Libya a kotun kasa da kasa (ICJ), Ahmed Al-Jahani, ya ce kotun da ke Hague ta amince da bukatar kasarsa na shiga shari’ar kisan kare dangi da Afirka ta Kudu ta shigar akan Isra’ila.
Al-Jahani ya shaidawa taron manema labarai cewa kotun ta ICJ ta amince da bukatar Libya.
Ya kara da cewa kotun ta ICJ ta kuma amince da bukatar wasu kasashe ciki har da Mexico na shiga cikin shari'ar.
Muna rokon Allah daya gaggauta kawo karshen Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila
