Ali Al-Qahoum, babban jami'in kungiyar Ansarullah da ke kasar Yemen ya ce "matukar Amurka ba kokarin faɗaɗa yaƙin take ba, dole ne ta kawo karshen goyon bayan da take badawa gurin mamayar Gaza da kuma killace ta.
Da yake zantawa da Al Mayadeen da sanyin safiyar Juma'a, Jami'in na Ansarullah ya ce ƙarin goyon bayan Amurka ga wuce gona da iri da yahudawan sahyoniyawan suke yi zai haifar da fadada fagagen hare-haren na Yaman.
Kalaman nasa na zuwa ne sa'o'i kadan bayan hare-haren da kawancen Amurka da Birtaniya suka kai kan Sanaa da Hudaydah, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane biyu tare da jikkata wasu 10.
Ya sha alwashin mayar da martani mai tsanani kan wadannan hare-haren.
Al-Qahoum ya ce tabbas Dole ne Amurkawa da Birtaniya sun san karfin Yemen, ya kara da cewa, makamai masu linzami na Yaman suna iya kai hari kan wuraren da yahudawan sahyuniya suke a cikin teku da kuma yankunan da aka mamaye.
