Kungiyar Hizbullah ta Kasar Labanon ta Murkushe Cibiyar Haduwar Sojojin Isra'ila


Dakarun Muslunci na kasar Labanon sun sake kai hari a cibiyar tarukan sojojin gwamnatin HKI a arewacin Palastinu da ta mamaye.


Kafar yada labaran Hezbollah a cikin wata sanarwa da ta fitar ta sanar da cewa: Mayaƙanta sun yi luguden wuta a kan taron mayakan 'yan mamayar a kusa da sansanin Jalul Alam da manyan bindigogi.


Kungiyar ta Gwagwarmayar Islama ta kasar Lebanon ta kara da cewa "mun kai hari kan sansanin Al-Ramtha da ke tsaunukan Kafr Shoba na kasar Lebanon da makami mai linzami wanda ya samu abin harin kai tsaye".


Ita dai wannan cibiyar ba ta yi karin bayani ba da kuma adadin wadanda suka mutu a harin.

Post a Comment

Previous Post Next Post