Kasashen nan masu kare Muradi da kuma Ra'ayoyin Kasashe masu Tasowa (NAM) ta mika sakon ta'aziyyarta ga al'umma da kuma Gwamnatin kasar Iran dangane da rasuwar shugaba Ibrahim Raisi da mukarrabansa ciki har da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian.
A cikin wata sanarwa da ta gabatar a zaman taron Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis, NAM, wadda a halin yanzu Uganda ke jagoranta, ta nuna girmamawa ga marigayi shugaban kasar Iran da mukarrabansa, wadanda suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin Iran a ranar 19 ga watan Mayu.
Sanarwar ta nuna goyon bayanta ga gwamnati da al'ummar Iran a wannan mawuyacin lokaci, tare da jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya, da ci gaba da hadin gwiwa tsakanin kasashe. Haka kuma ta amince da rawar da shugaba Raisi da ministan harkokin wajen kasar Abdollahian suka taka wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin Mambobin kungiyar ta NAM.
A karkashin jagorancinsu, Iran ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta hadin kai a tsakanin kasashe masu tasowa, kuma kudurinsu na yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban bai kau ba.
Sanarwar ta yi ta'aziyya ga iyalan shugaba Raisi da ministan harkokin wajen kasar Abdollahian da kuma al'ummar Iran wadanda suka yi rashin shugabanni biyu masu kwazo.
Wannan karimcin goyon baya daga NAM na nuni da irin mutuntawa da kuma jin dadin shugabancin Iran da irin gudunmawar da take baiwa al'ummar duniya.
