A wata budaddiyar wasika, Ayatullah Ali Khamenei ya yabawa daliban Amurka bisa Jajircewa da kuma Goyon Bayan da suke baiwa al'ummar Palastinu, duk da matsin lamba da suke fuskanta daga gwamnatinsu.
Ayatullah Khamenei ya yi karin haske kan tsawon tarihin wahalar da Palastinawa suke sha a karkashin gwamnatin Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila, tun daga kwace kasarsu zuwa yau. Ya yi Allah wadai da irin goyon bayan da gwamnatin Amurka ke baiwa Isra'ila, yana mai kiranta da Gwamnatin ta'addanci.
Jagoran ya yabawa daliban yadda suka hadu da sauran Duniya masu fafutuka gurin yaƙi da zalunci da kuma tabbatar da adalci. Ya kuma ja hankalinsu da su ci gaba da fafutukar da suke yi, inda ya kawo ayoyin kur’ani da suka jaddada tsayuwa ga abin da ya dace da kuma adawa da zalunci.
Wasikar Ayatullah Khamenei ta zo ne a matsayin nuna goyon baya ga daliban Amurkan da suke gudanar da zanga-zangar neman hakkokin Falasdinawa a cibiyoyin jami'o'i dake fadin Amurka. Wasikar ta jawo hankulan jama'a da mahawara, inda mutane da yawa ke yaba ta a matsayin wani gagarumin goyon baya daga babban shugaban duniya.
