Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya kira Jakadan kasarsa dake Isra'ila, Frederico Meyer, saboda yakin da Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza. Matakin dai wani koma baya ne a fannin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
Lula wanda ya yi kakkausar suka kan ayyukan Isra'ila a Gaza, ya kwatanta halin da ake ciki da kisan kiyashi, yana mai cewa, "Ba a taba ganin abin da ke faruwa a Gaza a tarihi ba, sai lokacin da Hitler ya yanke shawarar kashe Yahudawa."
An mayar da Meyer zuwa ofishin dindindin na Brazil a Majalisar Dinkin Duniya a Geneva. Wanda a halin yanzu babu Jakada a ofishin jakadancin Brazil dake Haramtacciyar Kasar Isra'ila.
Wannan mataki dai ya biyo bayan matakin da Colombia ta dauka na karya huldar diflomasiyya da Isra'ila a farkon wannan wata, inda shi ma shugaba Gustavo Petro ya kwatanta irin ayyukan da Isra'ila ke yi a Gaza da irin na kungiyar nan ta NAZI a Jamus.
Isra'ila ta kaddamar da yakinta na soji a Gaza bayan kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun kai wani samame na bazata a yankunan da ta mamaye.
Wanda hakan ya haifar da kashe mutane sama da 36,000, galibinsu mata da yara. Tare da kuma kewaye kusan gaba ɗayan Gaza, ta hanyar tare Abinci, magunguna, wutar lantarki, da ruwa da sauransu.
