Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya ce Iran ta samu nasarar tinkarar kamfen din matsin lamba na "Ikon shaidanun Duniya" a cikin shekaru arba'in da suka gabata.
Ya faɗa a yau Laraba a birnin Tehran cewa, mun yi nasara gurin tunkarar duk wani matsin lamba, sannan mun yi nasarar tabbatar da karfin al'ummarmu a kan makiya.
Babban hafsan IRGC ya bayyana cewa, juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979 ya yi kokarin yada manufofin 'yanci, da kuma martabar dan Adam a duniya.
Ya kuma ce "Muna so mu zama masu rike da tutar 'yancin wadanda ake zalunta daga bautarwar zamani.
Shaiɗanun Duniya sun san irin sauyin da aka samu a ikon duniya, wanda hakan zaya rage tasirin su a hankali a hankali, in ji Salami.
Wannan yasa suka dinga ɗaura Takunkumai kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kowane bangare, da suka hada da daukar matakan soja da takunkumin tattalin arziki, in ji shi.
