Wani Rahoto ya ce nan ba da Jimawa ba Gwamnatin Amurka za ta ba da sanarwar Turawa Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila makamai da suka Hada da Jiragen Yaki Samfurin F-15 na Dala Biliyan 18.
Jaridar Washington Post ta bayyana a cikin wani rahoto cewa gwamnatin Biden na shirin aika Bama-Bamai 1,800 masu nauyin kilogram 907 da kuma wasu bama-bamai 1,700 masu nauyin kilogram 227 zuwa Isra'ila.
Rahoton ya ce a baya an dakatar da samar da wadannan makamai saboda damuwar da Amurka ta nuna game da hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Rafah da ke kudancin zirin Gaza.
A cewar jaridar The Washington Post, wasu manyan 'yan majalisar dokokin jam'iyyar majalisar wakilai da dattijai sun ba da izinin sayar da makamai masu yawa ga Isra'ila, wanda darajarsu ta kai dala biliyan 18, biyo bayan matsin lamba daga gwamnatin Biden da kungiyoyin da ke goyon bayan Isra'ila. Wannan siyar ya ta haɗa da jiragen sama na F-15 guda 50.
Matakin dai ya biyo bayan kin amincewar da ‘yan majalisar suka yi, inda daga karshe suka samu matsin lamba daga bangaren gwamnati da kungiyoyin fafutuka, a cewar wasu jami’an Amurka uku da ke da masaniya kan lamarin.
Duk wannan bazai hana Isra'ila Rugujewa ba Insha Allah. Muna rokon Allah daya tarwatsa su da gaggawa.
