Anyi Amfani da Makaman Burtaniya Wajen Kashe Ƙananan Yaran Falasdinu da Basuji ba Basu Gani ba

 


Shugabar kungiyar agaji ta Oxfam mai hedkwata a Birtaniya, Halima Begum, ta yi Allah-wadai da sayar wa Isra’ila makamai da Birtaniyar ke yi, inda ta bayyana cewa, ana amfani da wadannan makaman ne wajen kashe kananan yaran Falasdinawa da iyayensu a Gaza.


A wata hira da tayi da jaridar The Guardian, Begum ta bayyana rashin jin dadin ta game da manufofin Birtaniya kan yakin Gaza, inda tace al'amarin ya saɓawa "hankali da ɗabi'a" ace London tana sayar da makamai ga Isra'ila a lokaci guda kuma tana bayar da agaji zuwa Gaza.


Begum wadda ta ziyarci Isra'ila da yammacin kogin Jordan da aka mamaye, ta jaddada cewa matakin da Birtaniya ta dauka ya saba wa tunani, tana mai cewa "Britaniya ta daina sayar da makamai ga gwamnatin Sahayoniya." Ta ce kamfanonin kera makamai na Burtaniya suna sayar da sassan makamai da ake amfani da su wajen kera makaman da ake kashe mutanen da basuji ba basu gani ba.


Ta kuma yi tambaya kan uzurin da gwamnatin Burtaniya ta bayar na cewa sayar da makamai 'lamari ne na kasuwanci' inda ta ce, "Idan da gangan kuke sayar da makaman da ake kashe dubban yara marasa laifi da kuma iyayensu, me ya sa za ku ci gaba?"


A cewar Oxfam, sama da Falasdinawa 37,000 ne aka kashe sakamakon mamayar da Isra’ila ta yi a Gaza, inda yara ke fuskantar tashin bama-bamai, rashin abinci mai gina jiki, da yunwa. Duk da wannan, gwamnatin Burtaniya ta gaza takaita ayyukan sojojin Isra'ila, lamarin da ya sa Begum ta koka da cewa "'Yan Adamtaka a cikin rayuwar nan tamu ya koma baya."

Post a Comment

Previous Post Next Post