Kafafen yada labaran HKI sun bayar da rahoton cewa wata kila kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuka ta ICC za ta fitar da hukuncin da ta yanke kan sammacin kame Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan yakinsa Yoav Gallant cikin kwanaki 10 masu zuwa.
A cewar rahoton safiyar ranar Litinin na kamfanin dillancin labaran IRNA ta kasar Iran, inda ta nakalto daga Al Jazeera, Tashar talabijin ta channel 13 ta HKI ta bayyana cewa, yiwuwar sammacin kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ya haifar da matukar damuwa ga Netanyahu yayin da yake yin shawarwari mai zurfi a kan hakan.
A cewar wannan rahoto, manyan masana harkokin shari'a a ma'aikatar harkokin wajen gwamnatin sun shagaltu da tattaunawa kan matakin da kotun Hague ta dauka.
A watan Mayun daya gabata ne, Babban mai shigar da kara na kotun ICC, Karim Khan, ya bukaci sammacin kama firayim ministan Isra'ila da ministan yakin kasar wanda hakan ya fusata gwamnatin sahyoniyawa da babbar mai mara mata baya, wato Amurka.
Khan ya bayar da hujjar cewa yana da dalilai masu ma'ana da zasu gamsar da cewa Netanyahu da Gallant "suna da alhakin aikata laifuka" na laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a Gaza.
Sai dai Netanyahu ya bayyana matakin da mai gabatar da kara na kotun ICC ya dauka a matsayin wauta yayin da gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta kira bukatar sammacin da "zalunci".
