Kungiyar Gwagwarmayar Islama ta Iraki ta sanar da kai wani sabon hari da makami mai linzami a wani muhimmin guri na HKI a tashar ruwan Haifa da ta mamaye.
A cewar IRNA inda ta nakalto daga kafofin yada labaran Iraqi, Kungiyar gwagwarmayar Islama ta Iraki ta fitar da wata gajeriyar sanarwa a jiya Asabar tana mai cewa mun Hari Haifa da makami mai linzami mai suna "Al-Arqib".
Gamayyar kungiyoyin gwagwarmayar Iraki sun gudanar da irin wadannan hare-hare da dama kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin ramuwar gayya kan yakin kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a zirin Gaza. A ranar Talatar makon da ya gabata ne kungiyar ta dauki alhakin kai hari tashar jiragen ruwa na Haifa da wani jirgi mara matuki.
A baya-bayan nan kuma, ta kai akalla hare-hare biyu na hadin gwiwa tare da dakarun kasar Yemen, inda ta kai hari kan wuraren da yahudawan sahyuniya suka mamaye a yankunan Falasɗinu.
Wannan kungiya dai ta sha nanata cewa za ta ci gaba da kai hare-hare kan wuraren makiya matukar dai ana ci gaba da zubar da jinin Falasdinawa.
A cikin watanni da dama da suka gabata kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Iraki ta kai hare-hare har sau 65 kan yankunan da Isra'ila ta mamaye.
