Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah dake Ƙasar Lebanon ta kai hari kan sansanin sojin Isra'ila da ke arewacin kasar Falasdinu da Aka Mamaye.
Kafofin yada labaran yaki na Hizbullah sun ɗaura bidiyon harin da aka kai kan sansanin gwamnatin sahyoniyawan da ke arewacin Falasdinu da ta mamaye da wani jirgi maras matuki.
Bidiyon ya nuna yadda kungiyar Hizbullah ta kai hari kan hedikwatar Bayad Blida mallakar sojojin gwamnatin sahyoniyawan kusa da kan iyakar Lebanon da jirgin mara matuki.
Wakilin Aljazeera ya ba da rahoton cewa an ji karar amsa kuwwa mai Alamta zuwan Makamai Masu Linzami a Saman Galilee, da ke arewacin Falasɗinu.
Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sha kai hare-hare kan sansanonin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a yankunan arewacin kasar a matsayin martani ga yakin kisan kare dangi da HKI ke yi a zirin Gaza.
