Hezbollah Tayi Amfani da Na'urar AI a Hare-Haren Jiragen Sama a Kan Isra'ila

 


Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta Kasar Lebanon tana amfani da Na'urar "Artificial Intelligence" a hare-haren da jiragenta maras matuki suke kaiwa kan sansanin sojojin Isra'ila, kamar yadda kafafen yada labaran Isra'ila suka ruwaito.


Rahotanni sun ce Hezbollah na amfani da Na'urar Artificial Intelligence (AI) don samar da dama ga jiragensu marasa matuka gurin kaucewa makamai masu linzami na sojojin Isra'ila a yankunan arewacin da suka mamaye, in ji rahotanni a ranar Asabar.


 Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da mayakan Hizbullah suna ta musayar wuta a kusan kowace rana tun bayan da gwamnatin mamaya ta fara kai hare-hare kan Falasdinawa a zirin Gaza.


Kwararru a fannin soji na Isra'ila sun yarda cewa kungiyar Hizbullah ta yi amfani da wani karamin bangare na karfinta na sama a kan Isra'ila.


 Tamir Hayman, wani Janar din Isra'ila mai ritaya wanda ya taba rike mukamin shugaban hukumar leken asiri ta gwamnatin kasar, yayi gargadi game da rugujewar karfin sojojin da ke fuskantar hare-haren kungiyar Hizbullah.


Ya kuma yi gargadin cewa ci gaba da rikici da kungiyar Hizbullah zuwa yaki, zai haifar da mummunan sakamako ga gwamnatin kasar, a daidai lokacin da aka mika kayan sojan ta a yakin Gaza.

Post a Comment

Previous Post Next Post