Iran Za ta mayar da martani idan Isra'ila Takai Wani Hari a Lebanon

 


Kafofin yada labaran gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun gargadi shugabanninsu a birnin Tel Aviv cewa idan har gwamnatin kasar ta kai wani gagarumin farmaki kan kasar Labanon to akwai yiwuwar Iran ta shiga cikin lamarin.


Wani mai gabatar da labarai na gidan talabijin na Channel 12 (Keshet 12) ya ce yakin da ake yi akan Gaza ya koya wa Isra'ila cewa kafin akai ga karshen yaƙi ana daukar lokaci mai tsawo, kuma ba abu ne mai yiwuwa kawo karshen lamarin cikin gaggawa ba.


Mai gabatar da labaran ya ci gaba da cewa, idan har jami'an Isra'ila suna tunanin yakin da za a yi a arewacin kasar (Ƙasar Falasdinu da suka Mamaye da ke kan iyaka da Lebanon), zai fi kyau a yi tambaya, idan ya kamata mu tafi yaki, muna da ikon kawo karshensa kuma nawa ake bukata don wannan?


Ya kara da cewa sojojin Isra'ila sun gaji kuma sun dogara gaba daya kan makaman Amurka, kuma gaba daya a cikin gida babu wata kariya, don haka ya kamata mahukunta su yi tunani da kyau kafin su yanke shawarar fadada yakin.


 Dana Weiss wani manazarcin siyasa na gidan talabijin na Channel 12 ya yi ishara da irin gagarumin farmakin da kungiyar Hizbullah ta kai kan sansanonin sojin Isra'ila da matsugunansu a arewacin Falasdinu da ta mamaye da kuma tuddan Golan da ta mamaye, inda ya ce Hotunan da muka gani a wannan mako a arewacin kasar mun damu matuka, sannan jami'an fadar White House suma sun damu saboda ba sa son ganin ana gwabza yaki a Arewaci.


Weiss ya bayar da hujjar cewa, idan aka fara yakin da ake shirin yi arewacin kasar, to tabbas a wannan karon Iran ba za ta yi shiru ba, akwai yiwuwar zata shiga cikin lamarin, kuma hakan zai sauya daidaiton yakin.


Tashar talabijin ta Kan 11 ta gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kuma bayar da rahoton cewa, adadin dakarun dake ajiye a cikin sojojin na Isra'ila ya karu zuwa dubu 300, kuma sojojin na neman a kara adadinsu domin yiwuwar kazamin yaki a yankin arewacin kasar.


Haka kuma, gidan rediyon Isra'ila ya ruwaito tun da farko cewa, majalisar ministocin wannan gwamnati ta yanke shawarar sake kiran wasu sojojin ajiyar su guda 50,000 da za su kasance cikin shiri idan har aka samu karuwar shiga fagen daga na Lebanon.


 A gefe guda kuma mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem a baya ya yi gargadin cewa idan har gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi yunkurin shiga wani gagarumin yaki, to Hizbullah a shirye take ta tunkari shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post