Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar cewa ta Ƙarar da wani bangare na sansanin sojin Saman Isra'ila na Meron da ke arewacin Falasdinu da ta mamaye ta hanyar amfani da makamai masu linzami.
Mayakan Gwagwarmayar Musulunci sun dauki wannan mataki ne domin tallafa wa al'ummar Palastinu da kuma mayar da martani ga harin da gwamnatin sahyoniya ta kai kan Jouya da ke kudancin kasar Lebanon, kamfanin dillancin labaran IRNA ne ya ruwaito hakan daga bayanan Hizbullah a yau Asabar
Tun daga farkon farmakin guguwar Al Aqsa kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a watan Oktoban shekarar 2023, kungiyar Hizbullah ta fara kai hare-hare kan gwamnatin ta 'yan mamayar a arewacin Falasdinu da ta mamaye.
Tun bayan barkewar yaki a Gaza sama da mutane 37,000 galibi mata da kananan yara ne aka kashe sakamakon hare haren ta'addancin Haramtacciyar Kasar Isra'ila.
