Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya gargadi "Isra'ila" da kada ta kaddamar da yaki a kan kasar Labanon, yana mai cewa yin hakan tamkar zuwa Jahannama ne ba tare da Dawowa ba.
Ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai tare da mai baiwa shugaban kasar Iraki shawara kan harkokin tsaro, Qasim al-Araji a birnin Bagadaza ranar Alhamis, yayin da fadan da ake gwabzawa a kan iyakar kasar Lebanon da yankunan da aka mamaye ke barazanar komawa yaƙi.
Bagheri Kani ya ce "Labanon za ta zama jahannama ba tare da komawa ba ga sahyoniyawan, kuma da su masu wayau ne, ba za su sake gwada Lebanon ba."
Kani ya ci gaba da cewa: "Isra'ila ta fara shan kashi mai ban mamaki a hannun Lebanon a cikin shekarar 2000 da kuma 2006."
Babban jami'in diflomasiyyar na Iran ya ce daidaiton Karfi ya canza tun a ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas mai hedkwata a Gaza ta kai wani harin ba-zata a kan 'yan mamayar, a matsayin ramuwar gayya akan "Isra'ila" saboda tsananta cin zarafin ta kan Falasdinawa.
Ya ce, "yahudawan sahyuniya na neman dawo da martabar su ta kafin ranar 7 ga watan Oktoba ta hanyar muzgunawa al'ummar Gaza, amma abin yaci tura".
Bugu da kari a ranar Alhamis, Bagheri Kani ya gana da firaministan Iraqi Mohammed Shia’ al-Sudani.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi kan batutuwan da suka shafi yankin nasu da kuma na kasa da kasa, daga ciki har da hare-haren "Isra'ila" kan zirin Gaza da kuma laifukan dabbanci da take aikatawa a yankin Falasdinu da aka yiwa kawanya.
Har ila yau, sun tattauna kan bukatar da kasashen duniya suke yi na yin kokari sosai don dakile harin "Isra'ila" da kuma hana yaduwar rikici a yankin.
Sannan kuma sun yi kira da a aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin Tehran da Bagadaza a fannonin makamashi, ilimi, sufuri da dai sauransu.
Sudani ya sake Jajantawa akan shahadar shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian da abokan tafiyarsu na hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a lamarin daya faru a watan jiya.
Ya kuma jaddada cewa, Iraki za ta ci gaba da karfafa alaka da hadin gwiwa da Iran.
A nasa bangaren, Bagheri ya mika godiyarsa ga kasar Iraki bisa sakon juyayin da ta yi kan shahadar jami'an Iran.
Ministan harkokin wajen na Iran na rikon kwarya, ya yaba da muhimmiyar rawar da Irakin ke takawa a yankin, da kuma yunkurin kasar na karfafa zaman lafiya a yankin.
