Kafofin yada labaran yahudawan sahyuniya sun ce wuta ta cinye kimanin mita 30,000 ta Ƙasa, sakamakon hare-haren makamai masu linzami da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai kan Yankunan Arewacin Falasdinu data Mamaye.
A cewar rahoton safiyar yau Alhamis na IRNA inda ta nakalto daga shafin yanar gizo na Aljazeera, jaridar Yediot Aharonot ta harshen Hebrew ta yi rubutu game da gobarar da ta kama filaye da dama a yankunan da aka mamaye bayan harba makaman roka daga kudancin kasar Lebanon a ranar Laraba.
Dangane da haka, Haaretz, wata jaridar Sahayoniya ta kuma rubuta cewa gobarar dake "arewacin Isra'ila" sakamakon rokokin da aka harba daga kudancin Lebanon barazana ce ga "kayan aiki masu mahimmanci".
A Jiya Laraba ne kungiyar Hizbullah ta harba makamai masu linzami kan wuraren Isra'ila domin mayar da martani kan harin da gwamnatin sahyoniyawan ta kai da dare, wanda ya yi sanadin mutuwar 'yan gwagwarmaya hudu ciki har da wani babban kwamanda, Sami Abdallah, a farmakin da Isra'ila ta kai kan wani gida a garin Jwaya a ranar Talata.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa, kungiyar Hizbullah ta harba rokoki 215 daga safiyar Laraba zuwa rana, inda wasu suka kai hari kan sansanonin soji, ciki har da bangaren leken asiri na sansanin soja na Miron da kuma masana'antar Bolsan dake da alaka da kamfanin soji na Rafael.
Masana'antar tana samar da kariya da kuma yin gyara ga injina na Sojojin yahudawan sahyoniya.
A ranar Talata, kungiyar Hizbullah ta ce ta harba makaman roka kusan 50 kan wuraren da Isra’ila a tuddan Golan da ta mamaye.
Kungiyar Hezbullah ta kasar Labanon ta kara kaimi wajen kai hare-haren Makamai Masu linzami da kuma Jirage Marasa Matuka akan sansanonin soja na gwamnatin sahyoniyawan a arewacin yankunan da ta mamaye a matsayin ramuwar gayya kan kisan kiyashin da take yiwa Falasdinawa, da kuma hare-haren da gwamnatin ke kai wa a yankunan da ke kudancin kasar Lebanon.
Ya zuwa yanzu, dubban gomomin yahudawan sahyoniya sun bar matsugunan da ke kusa da kan iyakokin kasar Labanon saboda fargabar hare-haren 'yan gwagwarmayan.
Muna roƙon Allah daya cigaba da ba 'Yan Gwagwarmayar Musulunci Nasara.
