Kafofin yada labaran kasar Lebanon sun bayyana cewa, kungiyar Hizbullah ta harba makamai masu linzami da rokoki da dama a wuraren da HKI ta Mamaye a Arewacin Falasdinu.
Tashar talabijin ta Al Mayadeen ta fada a ranar Laraba cewa an ji karar sautin amsa kuwwa mai Alamta zuwan Makamai bayan hare-haren da aka kai a arewacin Falasdinu data mamaye.
Kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya sun kuma bayyana cewa, kusan makamai masu linzami 30 ne kungiyar Hizbullah ta harba wadanda suka lalata gine-gine tare da haddasa gobara a sassa daban-daban na Qiryat Shemona.
Kungiyar Hizbullah a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce takai hari a kan wani barikin HKI a yayin harin.
Tun bayan kaddamar da farmakin yahudawan sahyuniya akan zirin Gaza ne dakarun Hizbullah suka fara kai hare-hare kan sansanonin yahudawan sahyuniya domin rage matsin lambar da HKI ke yi wa al'ummar Gaza.
