Sayyid Nasrallah Yace Har Yanzu Harin Al-Jalil yana kan Teburi

 


Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyed Hassan Nasrallah ya bayyana cewa, idan har aka kara ruruta wutar rikici, harin Al-Jalil zai cigaba da zama a kan Teburi.


Sayyid Nasrallah ya fada a ranar Laraba cewa, matakin soji, tsaro da kuma kare kai na Yahudawan sahyoniya na dab da durkushewa.  


Sayyid Nasrallah ya ce, tun daga ranar 8 ga watan Oktoba, makiya sun fahimci cewa, za a kai musu hari, inda ya yi alkawarin ci gaba da kai hare-hare kan wuraren yahudawan sahyoniya.


 Ya yi ishara da sabbin makaman na Hizbullah, yana mai cewa har yanzu ba su bayyana sabbin makamansu ba.


Muna da jirage marasa matuka masu yawa kuma muna kera makamai masu linzami da muke bukata, in ji shi.


 Ya kara da cewa kungiyar Hizbullah ba ta tsoron barazanar yahudawan sahyoniya kan kasar Labanon, kuma a shirye take gurin tunkarar kwanaki masu tsanani.


Sayyid Nasrallah ya gargadi kasar Cyprus kan taimakon sojojin yahudawan sahyoniya, yana mai cewa idan Cyprus ta bar Tel Aviv ta yi amfani da filayen tashi da saukar jiragen sama da sansanoninta wajen kai wa Lebanon hari, to itama zata kasance a cikin yaƙin.

Post a Comment

Previous Post Next Post