Yadda Sojojin Yemen Suka Kai Hari Kan Jirgin Ruwan "Tutor"





Gidan labarai na Al Jazeera ya fitar da wani faifan bidiyo na lokacin da sojojin Yaman suka kai hari kan wani jirgin ruwa mai suna "Tutor" a tekun Bahar Maliya, harin wanda aka kai a ranar 12 ga watan Yunin 2024, saboda karya dokar hana jiragen ruwa zuwa tashar jiragen ruwan yankunan Falasdinawa da aka mamaye.

Bidiyon wanda aka fitar a Jiya Laraba da Dare ya nuna karara cewa jirgin Tutor mai dauke da kwal mallakin kasar Girka an kai mashi harin ne da makami mai linzami da kuma wani Kwale-kwale maras Matuƙi da ke dauke da bama-bamai, lamarin da ya haifar da fashewa mai tsanani a kan jirgin.

A cewar IRNA, inda ta nakalto daga Aljazeera cewa, hukumar kasuwanci ta ruwa ta Birtaniya UKMTO ta tabbatar da nutsewar Jirgin a tekun da yammacin Talata tare da dora alhakin hakan akan sojojin kasar Yemen.

An bayar da rahoton cewa ma'aikatan jirgin sun yi watsi da jirgin ne bayan da aka harbo shi da makami mai linzami a ranar 12 ga watan Yuni kuma ya nutse a mako guda bayan haka, UKMOTO ta yi nuni da tarkace da kuma tabon mai a wurin da jirgin ya kasance na karshe.

Dukkanin ma'aikatan jirgin sun bar jirgin sai dai wanda ake kyautata zaton yana cikin dakin injin a lokacin da aka kai harin.

Tutor dai shi ne jirgin ruwa na biyu da 'yan Yemen suka nutsar bayan Jirgin Rubymar mallakin Birtaniya, wanda ke dauke da taki, wanda ya nutse a ranar 2 ga Maris, kimanin makonni biyu bayan harbin shi da makami mai linzami na sojojin Yemen.

 Kuma makon da ya gabata. Jirgin ruwan Verbena mallakar kasar Yukren mai dauke da tutar Palau, wanda ke dauke da katako a kan hanyarsa ta daga Malaysia zuwa Italiya, shima sojojin kasar Yemen sun kai mashi hari.

A halin da ake ciki kuma, wani jami'in kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya tabbatar a daren Laraba cewa, an kai farmakin kan jirgin ruwan Tutor ne da wani Kwale-kwalen bama-bamai, da makamai masu linzami guda biyu da jirage marasa matuka.

Jami'in da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa tashar talabijin ta Aljazeera cewa farmakin an kai shi kan Jirgin ruwa na wani kamfanin kasar Girka wanda ya sabawa dokar da kasar Yamen ta saka na hana jiragen ruwa zuwa tashar jiragen ruwa na gwamnatin sahyoniyawa a yankunan da ta mamaye.

Post a Comment

Previous Post Next Post