Gwamnatin Tarayya ta Canada, a wani Mataki na Nuna Adawa da Rikon Sakainar Kashi, ta Sanar da Cewa Za ta Sanya Kungiyar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) Cikin Jerin Ƙungiyoyin 'Yan Ta’adda.
A cewar IRNA, inda ta ambato jaridar Globe da kuma Jaridar Mail cewa, Ministan Tsaron Jama'a Dominic LeBlanc, da kuma cibiyoyin Demokaradiyya da Harkokin Gwamnati, sun yi magana game da sanya sunan IRGC a cikin Jerin Ƙungiyoyin 'Yan Ta'adda yayin wani taron manema labarai a ranar Laraba da Dare.
Ya ce Ottawa zata yi amfani da duk kayan aikin da take dashi don yaƙar ayyukan IRGC a Kanada.
A cikin watan Mayu, Majalisar Dokokin Kanada ta amince da wani kudiri na sanya IRGC, reshe na Sojojin Iran, a matsayin kungiyar ta'addanci.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanaani ya bayyana matakin da majalisar dokokin Canada ta dauka a matsayin rashin hikima.
Kanaani ya kuma yi Allah wadai da matakin da Kanadan ta ɗauka na sanya kungiyar IRGC cikin jerin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda, yana mai cewa matakin nasu kuskure ne kuma rashin da'a ne, kuma hakan ya faru ne sakamakon biyayyar 'yan siyasar Kanadan ga gwamnatin sahyoniya da kuma yin watsin su da ka'idojin dokokin kasa da kasa.
A cikin rahoton CBC ta ƙasar Kanada a ranar Laraba yayin da take ba da rahoto game da sanya IRGC a cikin Jerin Ƙungiyoyin 'Yan Ta'adda sun ce: Idan wata kungiya ta kasance cikin jerin ‘yan ta’adda na gwamnatin Tarayyar Canada, ‘yan sandan kasar na iya gurfanar da duk wani mutum ko kungiyar da ta bayar da tallafin kudi ko kayan aiki ga kungiyar. Bankuna kuma za'a iya daskare kadarorinsa''.
A cewar Kamfanin dillancin labaran reuters, ‘yan majalisar dokokin Canada sun dade suna kira da a saka kungiyar ta IRGC cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda, sai dai gwamnatin Liberal ta Firaminista Justin Trudeau ta kauracewa yin hakan, inda ta yi gargadin cewa hakan na iya haifar da sakamakon da ba'a yi tsammani ba.
Tuni Kanada ta saka Dakarun Quds wadanda wani bangare ne na IRGC a cikin kungiyar ta'adda. Kanada da Iran ba su da dangantakar diflomasiya tun 2012.
