Takaddama na Karuwa Tsakanin Netanyahu da Biden Inji Kafofin yada labaran Amurka

 


Kafofin yada labaran Amurka sun Bayyana cewa ganawar da aka yi a ranar Laraba tsakanin Amos Hochstein, mai taimaka wa shugaban Amurka da kuma Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Tayi muni Sosai.


 Shafin yada labarai na Axios ya ba da labarin ne ta hanyar ambato wasu bayanai da aka samu daga majiyoyin da ke da yuwuwar haifar da cece-kuce tsakanin Tel Aviv da Washington kan wani faifan bidiyo da Netanyahu ya fitar a ranar Talata.


A cikin faifan bidiyon, firaministan HKI ya yi ikirarin cewa Amurka na hana su tallafin soji, duk da bayanin Hochstein cewa zargin da yake yi na dakatar da Tallafin Makaman karya ne.


Axios ta naƙalto daga Jami'an kasar Amurka cewa, sabuwar takaddamar da ke tsakanin Netanyahu da gwamnatin Biden za ta hana yunkurin tsagaita bude wuta da kuma kaucewa yaki da kungiyar Hizbullah.


Yayin da labarin ya fito, tawagar Biden ta ce "sun fusata kuma sun kadu" saboda "rashin godiyar" Netanyahu.


Har ila yau, wasu jami'an Amurka da suka kalli faifan bidiyon zargin Netanyahu sun ce "ba shi da tabbas."


 A ranar Litinin din da ta gabata ne Ɗan Aiken Amurka ya tattauna da jami'an Isra'ila ciki har da Netanyahu gabanin ziyararsa birnin Beirut na Lebanon.


 Amurka ta sha yin kira da a sassauta zaman dar-dar a daidai lokacin da gwamnatin Sahayoniya da kungiyar gwagwarmayar Lebanon ke ci gaba da kai hare-hare tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza.


Sabbin al'amura sun zo ne yayin da shugabannin jam'iyyar Republican da Democrat a majalisar wakilai da na majalisar dattawa suka gayyace Netanyahu don yin jawabi a taron hadin gwiwa na majalisar a wata mai zuwa.


Tuni dai ‘yan majalisar da dama suka yanke shawarar kin halartar zaman.


Alexandria Ocasio-Cortez a yammacin ranar Talata tace ya kamata shugabannin jam’iyyar Democrat da na Republican su janye gayyatar da suka yi wa Netanyahu na yin jawabi a Majalisa a wata mai zuwa bayan daya fitar da wani faifan bidiyo da ke sukar gwamnatin Biden saboda ƙin bayar da makamai ga sojojin HKI.

Post a Comment

Previous Post Next Post