Kwamitin wasannin Olympic na kasar Iran (NOCI) ta bayyana ayarinta na wasannin Olympics na 2024 a birnin Paris na kasar Faransa da sunan "Khadem-ol Reza" domin girmama shugaba Ebrahim Raisi - shugaban kasar Iran na takwas wanda ya yi shahada a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar tunawa da ranar haihuwar Limamin Shi'a na takwas Imam Riza (AS) a ranar 19 ga Mayu.
A ranar 21 ga watan Mayu ne kwamitin zartaswa na NOCI ta yanke shawara kan sunan ayarin gasar Olympics, amma an ɗage taron zuwa mako mai zuwa bayan shahadar shugaba Raisi da mukarrabansa, kamfanin dillancin labarai na IRNA ne suka Ruwaito hakan a Ranar Litinin.
An zabi sunan ne domin tunawa da ayyukan da shugaba Raisi ya yi, shugaban hukumar ta NOCI Mahmoud Khosravi-Vafa ya bayyana a cikin wani shirin wasanni a Channel 3 ta tashar talabijin ta Iran.
Har ya zuwa yau, Iran ta yi nasarar samun kaso 34 a gasar Olympics ta 2024 da aka shirya yi a birnin Paris a watan Yuli.
