
Majalisar zartaswar kasar Iran ta gudanar da wani zama na gaggawa a ranar Lahadi don tunkarar wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin kasar wanda ya hada da shugaba Ebrahim Raisi da wasu manyan jami'an gwamnatinsa.
Mataimakin shugaban kasar Mohammad Mokhber ne ya jagoranci zaman da nufin hada karfi da karfe na gwamnati don gano jirgin saman mai saukar ungulu na Shugaba Raisi da tawagarsa a yankunan arewacin lardin Azarbaijan na kasar Iran.
Mokhber ya umurci ministan lafiya Bahram Einollahi da mataimakin shugaban kasa kan harkokin zartarwa Mohsen Mansouri da su je yankin da ake kyautata zaton jirgin ya fadi domin kula da ayyukan bincike da ceto a yankin.
Da sanyin safiyar Lahadi ne shugaba Raisi ke dawowa daga bikin kaddamar da madatsar ruwa a kan iyakar Iran da jamhuriyar Azarbaijan, lokacin da jirginsa mai saukar ungulu ya yi hatsari a lokacin da ya sauka a yankin Varzaqan.
An aike da tawagogi da dama zuwa yankin domin gano inda hatsarin ya faru. Har yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin bincike, amma jami'ai sun ce rashin kyawun yanayi na kawo cikas ga yunkurin.