Kungiyar gwagwarmayar Islama ta Iraki ta ce ta kai farmaki da jirage marasa matuka tare da kai hari kan muhimmin sansanin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a kudancin Palasdinu da ta mamaye.
Kungiyar ta Iraki ta fitar da labarin ne a cikin wata sanarwa da kafar yada labaran 'Yan Gwagwarmayar ta ruwaito, kamar yadda IRNA ta ruwaito a ranar Laraba.
Kafar yada labaran ta kara da cewa mayakan kungiyar gwagwarmaya ta Iraki sun kai hari kan sansanin da ke tashar jiragen ruwa na Eilat a daidai lokacin da suke tunkarar mamayar gwamnatin kasar, da taimakon al'ummar Gaza da kuma mayar da martani ga kisan gillar da gwamnatin mamaya ke yi kan al'ummar Palastinu.
Kungiyar masu fafutukar ta Islama ta yi gargadin cewa idan Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Gaza, za su kara gwabzawa ba tare da saurara waba.
A cewar kafafen yada labarai, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki ta kaddamar da hare-hare har sau 243 kan Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, a yankunan Falasdinu da ta mamaye da kuma tuddan Golan na kudu maso yammacin Siriya da aka mamaye tun farkon guguwar Al Aqsa a watan Oktoban shekarar 2023.
Tun farkon yakin Gaza, an kashe Mutane 35,000 wanda akasarin su yara da mata ne.
Allah yaba Al'ummar Fal
asdinu Mafita.
