Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kakkausar suka na kare Isra'ila daga zargin da ake mata na laifukan yaki, inda ya yi watsi da bukatar kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta sammacin kama shugabannin Isra'ila. Da yake magana a wani taron fadar White House jiya litinin, Biden ya jaddada cewa ba za a iya kwatanta Isra'ila da Hamas ba, kuma halin da ake ciki a Gaza bai zama kisan kiyashi ba.
Mai shigar da kara na kotun ICC, Karim Khan, na neman sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaro Yoav Gallant bisa zargin aikata laifukan yaki a yakin Gaza. Khan ya kuma bukaci a ba shi sammaci a kan wasu shugabannin Hamas uku kan laifukan yaki da cin zarafin bil adama.
Biden na shan suka akan kariyar da yake ba Isra'ila daga kungiyoyi masu goyon bayan Falasdinu, wadanda suka yi masa lakabi da "Kisan kare dangin Joe."
Sai dai shugaban na Amurka ya ci gaba da jajircewa wajen goyan bayansa ga Isra'ila, inda ya yi watsi da bukatar kotun ta ICC.
Matakin na kotun ta ICC dai ya janyo cece-ku-ce a tsakanin kasashen duniya, inda kasar Switzerland ke goyon bayan samun ‘yancin cin gashin kan kotun, ita kuma Rasha ta yi Allah wadai da matakin. Amurka na da damar da za ta tursasa kawayenta na Turai da su daina aiki da sammacin, saboda su ba mambobin kotun ICC ba ne.
Wannan ci gaban dai shi ne karon farko da kotun ta ICC ke neman shiga tsakani a rikicin yankin gabas ta tsakiya, bayan bayar da sammacin kama shugaban Rasha Vladimir Putin a watan Maris din shekarar 2023 kan zargin aikata laifukan yaki a Ukraine.
