
A yau Alhamis ne Kungiyar gwagwarmayar Musulunci dake kasar Iraki ta sanar da cewa dakarunta sun kai wani sabon hari da jiragen yaki marasa matuka a tashar jiragen ruwa na Eilat da Isra'ila ta mamaye.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a Iraki ta fitar da wata sanarwa a yau Alhamis inda ta sanar da cewa dakarunta sun kai hari kan wani muhimmin guri a tashar jiragen ruwa ta Eilat da ke kasar Falasdinu aka mamaye.
An dai kai wannan harin ne domin nuna goyon baya ga al'ummar Falasɗinu, wadanda ke karkashin yakin Isra'ila, da kuma mayar da martani ga laifukan da gwamnatin Tel Aviv ke Aikatawa.
Tun bayan fara aikin guguwar al-Aqsa a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata, dakarun kasar Yemen da kuma 'yan gwagwarmayar Musulunci na Iraki sun kai hare-hare a tashar jiragen ruwa ta Eilat da aka mamaye a lokuta da dama domin bayyana goyon bayansu ga al'ummar Gaza da ake zalunta.
A ranar 7 ga watan Oktoba ne gwamnatin yahudawan sahyuniya ta kaddamar da mummunan yakinta a kan Gaza.
A ranar 7 ga watan Oktoba bayan da kungiyar Hamas ta kai wani farmaki da ba a taba ganin irinsa ba a kan 'yan mamaya a matsayin ramuwar gayya kan yadda take muzgunawa al'ummar Palastinu.
Gwamnatin kasar dai ta kakaba wa yankin mai yawan jama'a kawanya, tare da katse man fetur, wutar lantarki, abinci, da ruwa ga Falasdinawa sama da miliyan biyu da ke zaune a wurin.