Sojojin Isra'ila sun janye daga sansanin Jenin bayan kisan kare dangi na kwanaki 2 da Sojojin suka yi

Sojojin Isra'ila sun fice a yau Alhamis daga sansanin 'yan gudun hijira na Jenin da ke arewa maso yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye bayan wani kisan kare dangi na kwanaki biyu da sojojin suka yi.

A lokaci guda tare da Janyewar sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila daga sansanin Jenin, asibitin Al Razi ya sanar da shahadar wani matashi sakamakon harbin da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila suka yi musu, in ji Al Jazeera.

A cewar Aljazeera, adadin shahidan Falasdinawa a Jenin a arewa maso yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye, ya kai mutane 12 a cikin kwanaki biyun da suka gabata.

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila da ke samun goyon bayan motocin soji da jirage marasa matuka sun kai hari a birnin Jenin kwanaki biyu da suka gabata inda suka fafata da Falasdinawa.

Allah (T) yaba Al'ummar Falasdinu Mafita, ya kuma kawo qarshen Isra'ila da duk masu goya masu goya mata baya a duk inda suke.

Post a Comment

Previous Post Next Post