Makaman 'Yan Houthi na Yemen Suna Kaiwa Har Bahar Rum, in ji Amurka

Houthis na Yemen na da makaman da za su iya kaiwa har zuwa tekun Bahar Rum, in ji wani babban jami'in tsaron Amurka.

Kamfanin dillancin labaran irna ya ruwaito inda suke dangantawa zuwa Bloomberg a yau alhamis cewa gwamnatin kasar Amurka ta damu da 'Yan Houthi na kasar Yemen da suke da karfin fadada hare-haren da suke kai wa jiragen ruwa daga tekun Bahar Maliya da Tekun Aden zuwa tekun Bahar Rum.

Wani jami'in da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa 'yan Houthis na da damar yin amfani da makamai masu linzami, kuma sun yi amfani da makami mai linzami na yaki da jiragen ruwa ta hanyar da ba a taba gani ba.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, Houthis sun bayyana aniyarsu ta fadada hare-haren da suke kai wa jiragen ruwan da ke kawance da gwamnatin sahyoniyawan da ke gabashin tekun Bahar Rum.

Al'ummar kasar Yemen sun bayyana goyon bayansu a fili ga gwagwarmayar Falasdinu ga mamayar Isra'ila tun bayan da gwamnatin kasar ta kaddamar da wani mummunan yaki a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba bayan da 'yan gwagwarmayar Palasdinawa na yankin suka kai wani harin ba-zata mai suna Guguwar Al-aqsa, kan 'yan mamayar.

Dakarun Yaman sun ce ba za su daina kai hare-hare ba har sai an kawo karshen hare-haren da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 35,562 tare da jikkata wasu 79,652

A cikin watan Disamba ne Amurka da Birtaniyya suka sanar da wani kawancen soji da za su kai wa kasar Yaman hari domin marawa gwamnatin sahyoniyawan baya

Muna roqon Allah daya cigaba da taimakon su tare da sauran 'yan gwagwarmayar Musulunci a duk Inda suke.

Post a Comment

Previous Post Next Post