
An yi jana'izar ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amirabdollahian wanda ya yi shahada, a hubbaren Abdul-Azim al-Hassani da ke birnin Rey a kudancin Tehran babban birnin kasar.
Jami'ai da kungiyoyin jama'a sun halarci bikin jana'izar da aka yi a yau Alhamis.
Kwanaki hudu kenan bayan Amirabdollahian tare da shugaban kasar Ebrahim Raisi da wasu jami'ai da dama suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin kasar Iran.
Mukaddashin shugaban kasa Mohammad Mokhber shi ma ya halarci taron. Ya kuma gana da iyalan marigayi babban jami'in Diflomasiyya, inda ya bayyana shahadarsa babban rashi ga kasar da ma'aikatar harkokin wajen kasar.
Tun da farko an kuma gudanar da wani biki a ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, wanda ya samu halartar manyan jami'anta.
A jiya Laraba ne al'ummar birnin Tehran suka yi bankwana da Amirabdollahian da sauran shahidan da suka yi hatsarin a yayin da dubban mutane suka halarci gurin.
Daga baya a ranar, da dama daga cikin manyan jami'ai daga wasu kasashe ma sun halarci taron tunawa da shahidan.