Iran ta fitar da Rahoto kan Hatsarin Jirgin sama mai saukar ungulu da ya Shahadantar da shugaba Raisi da Tawagarsa


Babban hafsan sojin kasar Iran ya fitar da wani rahoto kan hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da yayi sanadiyar Shahadar shugaba Ebrahim Raisi da tawagarsa. 

Rahoton ya yi karin haske kan lamarin daya faru a ranar Lahadin da ta gabata, inda jirgin da ke dauke da Raisi da tawagarsa ya yi hadari a arewa maso yammacin kasar Iran.

Jirgin mai saukar ungulu ya fado ne a lokacin da yake shawagi a kan hanyar da aka shirya shi, kuma bai kauce daga hanyar ba. 

Rahoton ya bayyana cewa jirgin mai saukar ungulu ya kama da wuta ne bayan ya fado a wani yanki mai tsaunuka, kuma tarkacen jirgin bai nuna alamun harsashi ko makamancin hakan ba.

Wata na'ura mai tashi sama da ba'a bayyana sunan taba ce  ta gano wurin da hatsarin ya afku, kuma ba da jimawa ba jami'an bincike suka isa wurin.

Sadarwar da ke tsakanin jirgin da sarrafawar ƙasa ba ta ƙunshe da wani abun zargi ba.

Za a sanar da al'umma game da duk wani binciken da aka samu nan gaba.

Muna roqon Allah daya karbi Shahadar su.

Post a Comment

Previous Post Next Post